Hukumomi a sassan jihohin da ke kudancin Amurka na ci gaba da kara nuna damuwa kan yadda ake samun karin wadanda ke kamuwa da cutar coronavirus a ‘yan kwanakin nan, yayin da rahotanni ke nuni da cewa Shugaba Donald Trump na watsi da al’amarin inda ya ke ikirarin cewa ba zai haifar da wata illa ba.
A yayin wata hira da aka yi da ita a shirin “This Week” na gidan talabijin din ABC, mai mukamin Magajin Garin birnin Phoenix da ke jihar Arizona Kate Gallego - (GAYEGO) ta ce “an yi hanzarin bude wuraren kasuwanci, bayan da aka rufe su a watan Maris da Afrilu.”
A cewarta, “an shiga wani yanayi mai sarkakiya,” yayin da aka samu mutum dubu 59 da suka kamu da cutar a birnin mai yawan mutum miliyan 1.7, ta na mai cewa yawan jama’a na fin karfin wuraren da ake zuwa yin gwajin cutar.”
Cikin ‘yan kwanakin da suka gabata, Amurka na ganin sabbin kamun cutar mutum sama da dubu 50, mafi akasari a jihohin da ke kudancin kasar, wadanda a watannin Maris da Afrilu suka yi nasarar kauce wa mummunar barkewar cutar a daidai lokacin da jihohin arewaci musamman New York ke fama da annobar.
Jihar Florida da ita ma ke kudu maso gabashin Amurka ta samu sabbin mutum dubu 11,400 a ranar Asabar 4 ga watan Yuli kadai, yayin da wasu manyan birane suka gudanar da bukuwan samun ‘yancin kai duk da cewa akwai wasu da suka soke gudanar da tarukan bikin gudun kada a yada cutar.
Magajin Garin Miami Francis Suarez ya fada wa gidan talabijin din ABC cewa, babu shakka, sake maido da harkokin yau da kullum da aka yi ne ya sa mutane suka koma yin cudanya, lamarin da ya sa aka ga karin wadanda suka harbu da cutar ta COVID-19.