Amurka: Mutum 21 Sun Kamu Da Coronavirus a Jirgin Ruwa

Fasinjoji a jirgin shakatawa na Grand Princess, yayin da wani jirgi mai saukar ungulu ke shawagi a samansa

Jami’ai a nan Amurka, sun ce an samu mutum 21 da ke cikin jirgin ruwan nan na yawon shatakawa dauke da cutar coronavirus, jirgin da ke can nesa da gabar tekun jihar California.

Sanarwar na zuwa ne yayin da adadin wadanda ke dauke da cutar ta coronavirus ya doshi dubu 100.

A jiya Juma’a mataimakin shugaban kasa Mike Pence ya ce suna aiki tare da hukumomin California domin a bar jirgin mai suna Grand Princess ya yada zango a wata tashar da ba a hadahada.

Hakan zai ba da damar a gwada dukkanin mutum dubu 3,500 da ke cikin jirgin, domin a ga ko suna dauke da cutar ta coronavirus.

Da farko an gudanar da gwajin ne akan wasu mutum 46 da ke cikin jirgin, bayan da wani jirgin soji mai saukar ungulu ya sauke kayan gwaje-gwajen cutar a dandamalin jirgin ruwan.

A dai jiya Juma’a shugaban Amurka Donald Trump ya sanya hannu kan wata doka da ta ba da damar a fitar da dala biliyan 8.3 domin daukan matakan yaki da cutar.