Amurka: Democrats Za Su Yi Zabe a Jihohi 14

Masu neman tsaya wa takarar shugaban kasar Amurka karkashin jam'iyyar Democrat, yayin wata muhawarar da suka yi wacce gidan talabijin ta CNN ta shirya.

Gasar neman tsaya wa dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Democrats ta fadada sosai a yau Talata, a daidai lokacin da masu kada kuri’a za su zabi ‘dan takarar da suke so a jihohi 14, domin nuna goyon baya ga wanda zai kara da Shugaba Donald Trump a watan Nuwamba.

Kusan kashi ‘daya cikin uku na daligate-daligate wadanda za su kada kuri’unsu lokacin zaben jiha-jiha na mai-rabo-ka samu-ne, ciki har da jihar California da ke yammacin Amurka da ke da manyan ‘yan takara.

Sanatan jihar Vermont Barnie Sanders shi ne ke kan gaba da daligate 58 ya zuwa yanzu.

Zai kuma iya samun kari daga masu kada kuri’a a jihohin California da Texas, inda zaben jin ra’ayin jama’a ya nuna shi ne ke gaban sauran ‘yan takarar.