Kasar Rasha ce ta yi tayin wannan tattaunawar, musamman ma da a yanzu da ta kara karfin sojanta a cikin kasar Syria.
Kerry wanda ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov a jiya Laraba, yana bukatar sanin niyyar Rasha.
Ya kuma ce ya gargadi Lavrov game da karuwar sa kan Rasha a lamarin Syria tare da marawa Bashar Al’assad baya.
Wanda yace, “Yin hakan zai kara ruruta wutar rikicin Syria da kuma zagon kasa ga bukatarmu ta fada da tsattsauran ra’ayi.”
Rasha dai ta aike da tankokin yaki, Mashawartan Sojoji, Kanikawa da jami’an tsaro zuwa Syria.
Da kudurin gina sansanin sojan sama a Latakia da ke kusa da teku, kuma garin da shi Al’assad ke da cikakken ikonsa.
Kamfanin dillancin labaran Rasha RIA Novosti ya ruwaito cewa, babban jami’in sojin kasar Nikolai Bogdanovski
ya ki musanta cewa ba barikin soja za su gina ba, amma a karshe yace komai na iya faruwa.