Gwamnatin Najeriya, ta wajen kamfanin kasuwancin man fetur na Najeriya wato NNPCL, tare da gwamnatin Amurka za su hada gwiwa wajen tabbatar da kawo karshen matsalar makamashi a kasar nan musamman ma samar da tsaftataccen iskar gas na amfani a gidaje, ababen hawa baya ga daukar matakan da suka dace wajen karę muhalli a Najeriya.
Shugaban kamfanin kasuwancin man fetur na Najeriya wato NNPCL, Mal. Mele Kyari ne ya bayyana hakan a a yayin ganawa da mataimakin sakataren makamashi na kasar Amurka, Geoffrey Pyatt, a wata ziyarar da ya kawo ma gwamnatin tarayyar kasar a birnin Abuja.
Geoffrey Pyatt shi ne jagoran tawagar gwamnatin Amurka da ta kawo ziyara Najeriya, inda ya bayyana cewa kasancewar tawagarsa a nan Abuja a yau, na nuni da irin yadda shugaba Joe Biden da gwamnatin Amurka ke daukar kawance da Najeriya, yana mai cewa fahimtarsu a game da matakan da kasar zata dauka a game da yadda za ta ci gaba da haɓaka albarkatunta ta hanyar da ƴan ƙasar za su ci moriyarsu baya ga bada karfi ga batun kare muhallin da ya hada kasashen duniya baki daya.
A nasa bangare babban sakataren ma'aikatar albarkatun man fetur ta Najeriya, Amb. Gabriel T. Aduda, ya ce komawa ga iskar gas shine sauyi ga amfani da makamashi a kasar kuma a shirye gwamnati ta ke ta karbi dukkan nau'i na taimako da haɗin gwiwa wanda za su bada gudunmuwa ga kasar wajen haɓaka amfani da iskar gas wanda kusan dukkan kasashen duniya suka amince da cewa shi ne mafi kyawun nau'in makamashi a cikin tsarin canjin da ake bukata a duniya.
Ambassada Gabriel Aduda ya kuma kara da cewa gwamnati ta rungumi wannan sauyin ne saboda irin nauyin da ya rataya a wuyarta ganin irin matakan da ta riga ta ɗauka don tabbatar da cewa Najeriya ta cika alkawuran da ta dauka na cire gurbataccen iskar carborn da ke yin illa ga muhalli kuma a shirye gwamnatin kasar take ta yi aiki tare da gwamnatin Amurka don ganin yadda za a iya hanzarta amfani da iskar gas a madadin man fetur ba kawai a cikin gidaje, ko a motoci ba, har ma da cimma nasara a cikin ajandar shekaru goma na tsarin iskar gas din kasar, kuma gwamnatin kasar na fatan cewa ƙwamitin aiki da za a kafa tsakanin Najeriya da Amurka zai mai da hankali sossai a kan wannan batun.
Saboda haka, a shirye gwamnatin Najeriya ta ke ta samar da wasu abubuwan karfafa gwiwa da za su taimaka wajen jawo hankulan masu zuba jari zuwa wannan fanni, ta yadda kasar zata iya hanzarta cike gibin da ke akwai ta fuskar samar da makamashi, in ji Gabriel Aduda.
Najeriya, wacce tuni ta kasance jagora ta fuskar siyasa da tattalin arziki a nahiyar Afrika, na neman yin jagoranci wajen aiwatar da matakan adalci da daidaito a ayyukan kawar da matsalolin sauyin yanayi, inda a yayin taron COP26 na Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi na shekarar 2021 kasar ta kuduri aniyar kawar da gurbatacciyar iska nan da shekarar 2060 karkashin jagorancin tsohon shugaba Muhammadu Buhari.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5