Amurka Da Faransa Sun Karrama Bukin Cika Shekaru 75

Shugabannin Amurka Da Faransa sun yi jawabin a wata makabarta da ake kira Colleville-sur-Mer.

Shugaban Amurka Donald Trump da shugaban Faransa Emmanuel Macron, sun jinjinawa zaratan sojojin da suka fafata a fagen daga, sun kuma jaddada muhimmancin hadin gwiwa, a tsakanin dakarun hadakar kasashen, a yayin da suka karrama bikin cika shekaru 75, da dakarun hadin gwiwa, suka kai farmaki, a lokacin yakin duniya na biyu, wanda ya kai ga samun nasara akan sojojin Nazi, da kuma kawo karshen yakin.

Shugabannin biyu sun yi jawabin ne, a wurin wata makabarta, da ake kira Normandy American Cemetery, dake Colleville-sur-Mer, inda aka birne sojojin Amurka fiye da dubu tara.

Macron, ya karrama wadanda suka sadaukar da rayukansu, kuma suka yi yakin neman 'yantan Faransa, shugabannin, sun fadi cewa, farmakin da aka kai a lokacin, ya canza makomar kasashen Turai, da duniya baki daya.

Macron, ya yi jawabinsa, da Faransanci, amma daga baya, ya sauya zuwa Turanci, a yayin da ya juya ga wasu sojoji, ‘yan mazan jiya, da suka zauna a bayan sa. Shi ma Trump, a jawabinsa, ya karrama wadanda suka "sadaukar da rayukansu, domin 'yan uwansu, da kasashensu, da kuma neman ‘yanci.