Yayin da China da Amurka suka koma kan teburin muhimmiyar tattaunawa a birnin Washington yau Alhamis, alamu na nuna cewa ta yiwu bangarorin biyu su cimma yarjejeniya.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bada rahoton cewa wasu manyan jami'an cinikayya daga bangarorin biyu na ƙoƙari cimma wasu manyan yarjejeniyoyi guda 6 da zummar warware wasu muhimman batutuwa masu zafi kama daga batun fasaha, da batun tallafin kasa, da kuma kutsen yanar gizo.
A farkon wannan makon, Shugaba Donald Trump ya ce babu rana ko lokacin da “za a cimma yarjejeniyar cinikayya, furucin da ya sa wasu ke gani kamar wa’adin ranar 1 ga watan Maris da aka sanya, wanda ta yiwu ya janyo karin haraji mai yawa daga kasashen biyu, a dage shi idan har aka sami ci gaba a ganawar da kasashen ke yi.