Manyan hafsoshin sojan kasar Afghanistan da kasashen dake makwaftaka da ita hade da na Amurka da NATO, sun yi taro yau Talata a birnin Kabul don tattauna hanyoyin yaki da masu safarar miyagun ababan sha masu sa maye da kuma kungiyoyin ta’addanci.
Kakakin ma’aikatar tsaro na Afghanistan Dawlat Waziri yace babbar manufar kiran taron itace don a san yadda za’a tunkari abubuwan dake haifarda kalubale ne ga sha’nin tsaron kasashen da abin ya shafa.
Shima babban hafsan hafsoshin sojan Pakistan, Janar Qamar Javed Bajwa, ya halarci taron inda kuma wakilan Amurka da na Afghanistan suka yi misa “taron dangi”, suna zarginsa da cewa kasarsa na bada mafaka ga mayakan Taliban, zargin da ya musanta, inda y ace rundunar sojan Pakistan ta jima tana farautar irin wadanan mayakan.