Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Hallaka Jami'an Leken Asirin Tsaron Kasar Afghanistan 16


Shugaba Ashruf Ghani na Afghanistan
Shugaba Ashruf Ghani na Afghanistan

A wani al'amari mai kama da canza sheka ko kuma munafukar dabara, wasu daga cikin jami'an leken asirin tsaron kasar Afghanistan sun bindige abokan aikinsu 16 sannan su ka canza akida ko kuma su ka koma ainihin inda su ka fito, wato kungiyar Taliban.

Jami’ai a Afghanistan sun ce wasu jami’an leken asirin tsaron kasa su hudu, sun bindiga abokan aikinsu guda 16 sannan su ka tsere su ka shiga kungiyar ‘yan tawayen Taliban, a lardin Helman da ke Kudancin kasar.

Wannan al’amari mai daure kai, na harin dan ciki, ya auku ne da dare a sansanin Hukumar Tsaron Kasa NDS a takaice da ke gundumar Gerishk, abin da majiyoyi su ka gaya ma Muryar Amurka Kenan a yau dinnan Lahadi.

Mai magana da yawun gwamnatin lardin, Omar Zawak, ya tabbatar da aukuwar lamarin sannan ya kara da cewa Taliban ta kuma kai samame a cibiyar ta NDS a matsayin sharar fagen harin cikin, al’amarin da ya haddasa fada mai tsanani da dogarawan tsaron Afghanistan.

Zawak ya ce duka bangarorin biyu sun yi asarar rayuka masu yawa to amma bai yi karin bayani ba.

Magoya bayan Taliban ko kuma ‘yan Taliban da kan shiga soji ko zama ‘yan sandan kasar a munafurce, kan kai harin ciki daga loto zuwa loto, to amma hakan bai cika faruwa a wurare irin hukumar NDS ta kasar ta Afhanistan ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG