Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry wanda yake ganawa da shugabannin kasashe da suke yankin Gulf a Saudiyya,jiya Alhamis, yayi kokarin ya kwantar masu da hankalin kan yarjejeniyar da ake shirin kullawa kan shirin Nukiliyar Iran, cewa "Amurka ba zata kauda ido kan take-taken Iran a yankin Gabas ta Tsakiya ba.
A daren Laraba ne Kerry ya isa Riyadh, bayan kwanaki uku yana shawarwari da ministan harkokin wajen Iran Mohammed Javad Zarif a Switzerland, da zummar cimma jadawalin yarjejeniya kan shirin Nukiliyar Iran din kamin nan da 31 ga wannan watan.
Kawayen Amurka a yankin na Gulf, musamman kasar Saudiyya, tana nuna damuwar cewa yarjejeniyar ba zata hana Iran cigaba da neman gina makaman nukiliya. Kuma ta damu cewa sassauta takunkumi kan kasar Farisar zai sa ta sami sukunin katsalandan cikin harkokin cikin gidan wasu kasashe da suke yankin.
Mr. Kerry ya gayawa manema labarai a Riyadh cewa "duk da shawarwarin da muke yi da Iran kan shirin Nukiliyarta, ba zasu kauda kai daga take-taken Iran na wargaza al'amura a kasashe kamar Syria, da Lebanon, da Iraqi, da kuma zirin Arabia musammanYemen".
Daga bisani Mr. Kerry ya gana da sarki Salman na Saudiyyan.