A Jiya Alhamis sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, ya fadi cewa Amurka ba ta da niyyar sassauta takunkumin da ta garkamawa Koriya Ta Arewa har sai ta tabbatar da cewa Koriyar ta rage barazanarta matuka, a matsayin kasar da ta mallaki makaman nukiliya.
Koriya Ta Arewa ta ce takunkumin da Amurka ta sanya ma ta na cikin dalilan da suka janyo abinda ta kira “matsalar abinci” a kasar. Koriyar na kuma bukatar a sassauta mata takunkumin bayan haka ta na kuma yin kira ga Majalisar Dinkin Duniya akan ta agaza mata da abinci.
Majalisar Dinkin Duniya ta fadi cewa kashi 41 cikin dari na al’ummar Koriya Ta Arewa ba su da isasshen abincin da zasu ci.
Wadannan kalaman na sakatare Pompeo na zuwa ne mako daya kafin taron koli na biyu da za a yi tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da shugaban Koriya Ta Arewa Kim Jong Un a birnin Hanoi dake kasar Vietnam.