A wani jawabi da ta gabatar daga jami’ar Michigan dake Amurka ga mahalarta taron, babbar jami’a dake lura da shirin hadin gwiwar na kasar Amurka Dakta Saweda Liverpool, ta ce shirin na daya daga cikin tallafin da Amurka ke bayarwa ga kasashen waje da kuma shirin gwamnatin Najeriya na maida kasar mai dogaro da kai ta fuskar abinci.
Bugu da kari jami’ar Michigan da tayi suna wajen koyar da aikin gona a Amurka, inda kuma ta bada gurabe ga dalibai dake nazarin fannin noma don zuwa Amurka domin samun horo na zangon karatu rabin shekara ga masu karatun digiri na biyu da kuma shekara guda ga masu karatun digirin digirgir wato dakta.
Dakta Baba Abdullahi malami ne a sashen aikin noma a jami’ar Ahmadu Bello Zaria, ya ce samar da abinci shine kashin bayan kowace kasa, kuma matakin gwamnatin amurka na tallafawa Najeriya abin yabawa ne matuka, wanda ya zama abin koyi ga sauran kasashe. Ya ce dole ne a samu horoswa ta zamani kafin kudirin gwamnati ya samu nasara a wannan fanni.
Wasu daga cikin dalibai kuma malaman nazarin aikin noma da zasu ziyarci Amurka domin samun horon, sun hada da malama Fatima sule daga jami’ar Ibbu dake jihar Niger, wadda itace daliba guda mai karatun digirin digirgir kacal daga Arewacin Najeriya, ta yaba da matakin gwamnatin Amurkan da Najeriya na tallafawa harkar noma domin dogaro da kai, tare da karatu tukuro domin baiwa mara da kunya a lokacin karatun nasu.
Batun samar da wadataccen abinci dai ya kasance daya daga cikin kudirorin gwamnatin najeriya maici yanzu, wato na maida kasar mai dogaro da kai ta fusrkar abinci.
Domin karin bayani saurari rahotan Babangida Jibrin.
Your browser doesn’t support HTML5