Shugaban kwamitin fidda gwani Khalil Bolaji na zaben dan takarar gwamnan Sokoto shi ya bayyana Aminu Tambuwal a matsayin wanda ya lashe zaben.
'Yan takara biyar suka fafata da kakakin majalisar. To amma kakakin Aminu Tambuwal ya basu tazara da yawan gaske. Ya samu kuri'u dubu uku da dari hudu da sittin da shida. Shi kuma Sanata Dahiru Umaru Tambuwal ya samu ashirin da uku. Yasha'u kuma ya samu kuri'u goma sha uku, yayin da Barrister Abubakar Sanyinna da Farfasa Muhammed Bashar suka tashi ba ko kuri'a daya.
A cikin murna da farin ciki Aminu Waziri Tambuwal yayi alkawarin yin aiki da wadanda ya kayar a zaben. Ya kirasu su zo su hada kai domin su gina jihar tare. Yace da yaddar Alla kowannensu zai yi masu adalcin tafiya tare ba tare da nuna banbanci ba. Yace babu banbancin bangaranci ko na jinsi.
Amma wasu daga cikin 'yan takarar sun yi korafin rashin adalci a wurin gudanar da zaben. Dalili ke nan da ya sa Sanata Umaru Dahiru Tambuwal da Barrister Aliyu Sanyinna suka fice daga wurin zaben tun kafin a gama. Barrister Aliyu ya fice ne daga filin bayan ya wanke wani dan majalisar wakilai da mari.Salihu Bashar Kalanjeni shi ne Barrister Aliyu ya mara.
Lamarin ya ja hankalin gwamnan jihar Aliyu Magatakarda Wamakko lokacin da yayi jawabi a karshen zaben. Wadanda suka fice idan domin jama'ar Sokoto suke yi su dawo su goyi bayan wanda Allah ya ba, inji gwamnan. A hada karfi a gina jihar Sokoto.
Sauran 'yan takaran sun yi muba'aya ga Aminu Waziri Tambuwal.
Ga rahoton Umar Sanyinna.
Your browser doesn’t support HTML5