Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Sunan Dan-Takarar Gwamna a Cikin Kundin Ragistar Jam'iya


Yayin da ake gudanar da zaben fidda 'yan takara yau Alhamis, wata danbarwar siyasa na kunno kai a jam'iyyar APC.

Wata dambarwar siyasa ta kuno kai a jam’iyar adawa ta APC a jihar Naija. Alh. Mustapha Aliyu Wushishi yana cikin daya daga cikin ‘yan takara uku da ke neman a tsayar da su takarar gwamnan jihar. Yace jam’iyar bata yi musu adalci ba, kasancewar ya sai form na shiga takarar, kuma ya canza sheka zuwa jam’iyar da magoya bayanshi sama da mutane dubu gona 10,000. A cewar Alh. Isma’ila Modibbo Tagina sakataren tsare tsare na jam’iyar APC a jihar Naija, yace basu ma san da zamanshi a cikin jam’iyar ba.

Kuma cewar da yake yi ya siya form na shiga takara, su basu san da ya yi hakan ba don basu gani ba a cikin asusun uwar jam’iya ba. A takaice ma mun duba kundin ragista na karamar hukumar da yace yafito amma ba muga sunanshi ba a ta bakin sakataren jam'iyyar.

Shi kuwa jami’in yada labarai na kungiyar a jihar Mr. Jonathan Batsa ya bayyana mafita dangane da wannan dambarwar, ya kamata shi Alh. Wushishi da sauran magoya bayansa da su dawo don a hada hannu a ceto wannan jam’iyar a jihar Naija.

Babu Sunan Dan-Takarar Gwamna a Cikin Kundin Ragistar Jam'iya - 3'11"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG