Aminu: Manyan Jam'iyyun Siyasa Sun Yi Kaka Gida

Dan takarar majalisar tarayya daga karamar hukumar Tarauni, karkashin jamiyyar ADC, wanda ke cewa, har yanzu akwai karanci wayewar kai dangane da yadda harkokin siysar Najeriya ke wakana.

Aminu Muhammad Malami, matashin dan siyasa ne wanda ya ce manyan jam'iyyun siyasa guda biyu, wato Jam'iyyun APC da PDP, basu bawa kananan jamiyyu dama, domin kuwa a cewarsa ta inda za’a gane cewar ana damawa da matasa shine, a lokacin ba da mulki ko yunkurin haka, muddin zaka bawa matasa dama, toh akwai tabbacin cewar za’a dama da matasa.

Amma akasin hakan ne a ke gani a yanzu, domin ko a kwamitin ba da mulki a matakin jihar, matasa da ke cikinsa mafi karancin shekaru 'yan shekaru 40 ne, wanda bai nuna cewar akwai yunkurin damawa da su ba.

Har yanzu tunda ba’a fara rabon mukaima ba don haka ba za’a karas ba, ko za’a dama da su ko akasin haka, amma masu iya magana kan ce Juma’ar da zata yi kyau tun daga Laraba ake farawa, don haka har yanzu babu wani yunkurin sanya matasa a wasu kwamitoci na mika mulki.

Ya ce tunda an dan samu kurkuse na jefa matasa a wadanan kwamitoci, toh matasa na fata cewar za’a gyara a wajen bada mukamai a nan gaba, domin cika alkawarin da aka daukar wa matasa.

Your browser doesn’t support HTML5

Manya Jam'iyyun Siyasa Basu Bawa Kananan Jam'iyyu Dama: Aminu Muhammad Malami 03'53"