Zaburar ruwan tuke a fadin duniya zata karu da kimanin inci 27 zuwa 4, koda kuwa gwamnatocin kasashen duniya sun cika alkawarinsu na kawo karshen amfani da man fetur, biyo bayan yarjejeniyar magance matsalar dumamar yanayi da aka cimma a taron kasar Paris.
Matakan gaggawa zasu taimaka matuka wajen magance matasalar dumamar yanayi, musamman idan aka dauki sabon tsarin ‘Greenhouse Emissions’ wajen amfani da sababbin sinadaran makamashi.
Masana na ganin cewar, wannan tsarin zai kawar da matsalar dumamar yanayi har na fiye da shekaru 200. Anbaliyar teku na barazana ga biranen Shanghai da birnin Landon.
Tsaunin kankara dake cikin manyan teku a fadin duniya suna narkewa sanadiyar dumamar yanayi, wada hakan zai kara yawan ruwa dake kwarara cikin tekun Maldive da tekun India. Rahotanni sun bayyanar da cewar nan da shekarar 2300, za’a samu karuwar ambaliyar teku, koda kuwa gwamatocin sun bi ka’idojin da aka shata.