Ambaliyar Ruwa ta Kwashe Gidaje Sama da 200 a Jihar Zamfara

Wani Wajen Da Ruwa Yayi Ambaliya

Sama da gidaje 200 ne suka lalace sanadiyyar ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a karamar hukumar Maru dake jihar Zamfara.

Lamarin dai ya uku ne a daren jiya Talata a lokacin da aka tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya, ruwan da ya malala daga wata babbar gada dake kan babban titin Sokoto zuwa Gusau a garin na Maru.

Ruwan dai ya mamaye gadar ya kuma Malala zuwa gidajen dake kusa, daga bisani ya kuma mamaye wasu daruruwan gidaje a cikin garin na Maru.

Mazauna garin na Maru sun bayyana yadda lamarin faru, suna fadin cewa basu taba ganin ruwan sama irin wannan ba. Sun kuma yi kira ga gwamnati, da hukumomi akan su taimaka masu da agajin gaggawa domin wasu ko tsinke basu tsira da shi ba.

Babu dai rahoton mutuwa ya zuwa lokacin da aka hada wannan rahoton amma an sami hasarar dukiyoyin kuma iyalai da yawa sun rasa matsugunnansu.

Shugaban karamar hukumar mulki ta Maru, Salisu Isa, wanda ya kai ziyara wajen domin ganewa idonsa abinda ya faru, ya bayyanawa Murtala Faruk, wakilin sashen hausa cewa, sun kafa wani kwamitin wanda zai yi kiyasin gidajen da ambaliyar ta shafa da kuma hasarar da aka yi domin sanar da gwamnan jihar.

Ya kara da cewa yanzu suna kokari su ga irin tallafin gaggawan da jama’ar ke bukata. Bayan hasarar gidaje da dukiyoyin, ambaliyar ta kuma lalata wani sashe na gadar da kuma babban titin na Sokoto zuwa Gusau.

Ga karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Ambaliyar Ruwa ta Kwashe Gidaje Sama da 200 a Jihar Zamfara - 2'54"