Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutum Kusan 20 A Karachi Babban Birnin Pakistan
Your browser doesn’t support HTML5
Mahukunta sun ce ruwan sama kamar da bakin kwarya ya sauka a Karachi, babban birnin Pakistan. Bala'in ya rutsa wasu yankuna ya kuma kashe mutane kusan 20. Lamarin da ya tilasta hukumomi yin amfani da kwale-kwale don fidda wadanda suka makale tsakanin tituna da cikin gidaje sakamakon ambaliyar.