Lamarin ya jawo kiraye kiraye ga hukumomi su kawo agajin gaggawa don tallafawa jama'a da su ka tabka asarar dukiyoyin su, har ma da rayuka.
Ya zuwa yanzu mutum 108 ne su ka rasa rayukansu a jihohin Kebbi, Kano, Jigawa, Imo da sauran su.
Tun shigowar damunar bana, hukumar kula da yanayi ta tsinkayo samun ambaliyar ruwa tare da baiwa gwamnatoci da al’umomi shawarar dau matakan da suka dace.
Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu ya zaga yankunan da ambaliyar ta yi awun gaba da gonaki inda ya ce, gwamnati ta dau matakan tallafawa wadanda lamarin ya shafa.
Isa Ramin-Hudu Hadeja mai rubutu ne a yanar gizo ya ce, dattawa sun ce an shafe dogon zamani ba a ga irin wannan ambaliyar ba.
Gwamna jihar Jigawa Muhammadu Badaru Abubakar ya ce, gwamnati ta kai tallafin farko ga al'umma.
Don tsanantar lamarin Sultan Muhamnad Sa'ad Abubakar ya bukaci gwamnatin taraiya ta kara azama wajen ragewa mutane radadin da su ka shiga.
Damuna ta fara janyewa da hakan ke rage barazanar sabuwar ambaliyar, inda hakan ya ba da sarari ga mutane lissafa asara da alherin da akasin ya haddasa mu su.
Saurari cikakken rohoton Nasiru Adamu El-hikaya cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5