Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Ta Ke Ranar Matan Karkara Ta Duniya


NIGER: Matan karkara
NIGER: Matan karkara

Majalisar Dinkin Duniya ta kebe ranar 15 ga watan Oktoba na kowacce shakara a zaman ranar matan karkara ta duniya.

Ranar matan karkara ta duniya, rana ce da a ke maida hankali wajen haska fitila a kan matsalolin da suka addabi mata dake zaune a yankunan karkara.”

A bana an gudanar da bukin ne da taken, “Matan karkara da ‘yammata da suke kara jajircewa.” Majalisar Mata tana amfani da wannan dama wajen yin kira da a dauki matakan da zasu kai ga ba mata da ‘yammata damar cimma gurinsu na rayuwa.

kaddamar-da-bukin-karrama-mata-a-fadin-duniya

niger-na-tunawa-da-ranar-tsara-haihuwa-ta-duniya

yau-ce-ranar-mata-ta-duniya

Majalisar ta ce za a iya yin haka ne ta wajen ba matan damar da za su iya ci gaba a zamanin da ake fuskantar sauyin yanayi, su iya kara ci gaba a fannin harkoki noma da samun isasshen abinci da kuma albarkatun kasa, bisa la’akari da cewa, inda matan karakara suka fi karfi ke nan.

Matan karkara
Matan karkara

An fara kiyaye ranar matan karkara ta duniya ne a shekara ta 2018 bayanda Taron Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kudurin doka mai lamba 62/136 da aka tsayar ranar 18 ga watan Disamba shekara ta 2007 wadda ta jadada muhimmancin gudamuwar da matan karkara suke badawa a harkokin noma da samar da abinci, da kuma yakar talauci.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, matan karkara suna bada gagarumar gudummuwa ga tattalin arzikin yankunan karakara da kuma kasashe masu tasowa har ma da kasashen da suka ci gaba. Bisa ga cewar Majalisar Dinkin Duniya, matan karkara suna bada gudummuwa ga ayyukan noma a gonaki, da kiwo, da sarafffa albarkatun gona, da girki da diban ruwan, da dai sauran ayyukan kula da iyali da suka hada da renon ‘yayansu da kula da marasa lafiya da kuma tsofaffi.

Wata mata tana saida kayan lambu
Wata mata tana saida kayan lambu

Sai dai ranar ba ta wani tasiri ga galibin matan karkara wadanda da dama ba su san ma da ranar ba balle ganin a zahirance an dauki matakin inganta rayuwarsu.

A halin da ake ciki kuma, wani sabon rato na nuni da cewa, yunwa da rashin abinci mai gina jiki nata kara ta’azzara a wasu yankunan nahiyar Afirka saboda annobar coronavirus, musamman ma a yankunan al’umomin dake fama da talauci ko wadanda rikicin dake ci gaba ya rutsa da su, a cewar wani zaben jin ra’ayi da mutane 2,400 a kasashen Afirka 10 da kungiyar agaji ta kasa da kasa ta Red Cross ta gudanar.

Binciken da aka gudanar daga watan Yuni zuwa Agusta, ya nuna cewa annoba ta haddasa rasa ayyuka da kuma hana mutanen damar yin noma ko zuwa kasuwanni.

Tun farkon annobar, kashi 94 cikin 100 na mutanen da aka ji ra’ayinsu sun bada rahotan cewa farashin abinci da sauran kayyayakin amfani na yau da kullum ya karu, yayin da kashi 82 cikin 100 suka ce sun rasa ayyukansu ko kudaden da suke samu. Kashi 7 cikin 100 kadai ne suka ce sun tara kudin da ishesu cikin annoba.

A yammacin Afirka, a Najeriya inda tashin hankalin ya addabi arewa maso gabashin kasar, adadin yaran da aka kula dasu ta hanyar shirin abinci mai gina jiki ya karu da kashi 20%, yayin da yawan masu fama da rashin abinci mai gina jiki ya karu da kashi 10% idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG