A yau Litinin an kwashe kusan mutane 1,500 bayan da Rafin Seine da ke Birnin Paris ya tumbatsa ya karu da takun mita hudu, sama da yadda zurfinsa yake, bayan da aka yi ta tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya a cikin watan nan na Janairu.
WASHINGTON DC —
Ruwan saman, ya haifar da barna a sama da garuruwa 240, wadanda ke gabar Kogin.
Ruwan ya karu ne da yawan meter 5.84 a kan ma’aunin Austerlitz, sama da abinda aka yi hasashe a makon da ya gabata, wanda ya kuma ya gaza yawan meter 8.62 da aka gani a shekarar 1910.
Ana sa ran wannan karuwa da Rafin na Seine ya yi, zai ci gaba da zama a haka a baki dayan yinin yau Litinin.
Amma kuma ana sa ran zai sauka izuwa gobe Talata, yayin da kuma mahukunta ke cewa za a kwashe makwannin da dama, kafin a share dattin da ruwan ya bari a babban Birnin kasar ta Faransa.
Sanadiyar wannan bala’i, an rufe wasu hanyoyi a Birnin na Paris, aka kuma dakatar da zirga zirgar kwalekwale da ke zirga zirga a Rafin.