Shugaba Buhari ya bayyana kokarin da gwamnantinsa ke yi na sake tsugunar da 'yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya daidaita.
An aiko da agajin ne da sunan shugaban kasa domin a rabawa wadanda bala'in ambaliyar ruwa ya shafa domin rage masu radadin hasarar da suka yi.
A cewar mai magana da yawun gwamnatin jihar Adamawa yace an samu nasara akan 'yan ta'ada na Boko Haram saboda an kwato yawancin wuraren da suka mamaye.
Gwamnan jihar Adamawa Sanata Bindow ya yabawa gwamnatin tarayya saboda tallafin da ta baiwa jihar. Ya bayyana abubuwan da gwamnatin ke yi amma ya ce akwai wasu ayyuka da suka fi karfin gwamnatocin jihohin da Boko Haram ta daidaita wato Adamawa da Borno da Yobe saboda haka ya nemi gwamnatin tarayya da ta taimaka masu.
Jihar Adamawa na bukatar nera biliyan ashirin da zata iya taimakawa wadanda rikicin Boko Haram ya shafa. Kudaden zasu taimaka wurin sake ginawa masu gidajensu da makarantunsu da asibitocinsu da mijami'u da masallatai da ma kasuwanni.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5