Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojin Najeriya Ta Bayyana Hotunan 'Yan Ta'ada Dari da Ake Nema


Hafsan Sojojin Najeriya Janar Tukur Buratai
Hafsan Sojojin Najeriya Janar Tukur Buratai

Bayan kammala taron kwanaki uku da sojojin Najeriya suka yi a Maiduguri a karkashin hafsansu Janar Buratai sun fitar da hotunan mutane dari da suka kira 'yan ta'ada

Hafsan sojojin Najeriya Janar Buratai shi ya kaddamar da hotunan mutane dari da aka kyautata zaton 'yan ta'adan Boko Haram ne kuma ana nemansu ruwa a jallo.

Janaran ya bada wasu lambobin wayar tarho da yace duk inda aka ga kowane daga cikinsu a kirawosu a sanardasu.

Janar Buratai ya yi karin haske akan makasudin taron nasu. Yace sun yi taron ne saboda wayarwa jama'a kai domin yakin da suke yi da 'yan ta'ada. Yace suna neman goyon baya unda yakin bana sojoji ba ne kawai.

Ya kira duk 'yan Najeriya su goyi bayan wa'adin da shugaban kasa ya ba sojoji na kawo karshen kungiyar Boko Haram da ta'adanci.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:25 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG