Amaju Pinnick Ya Yi Nasara Da Gagarumin Rinjaye

An zabi Amaju Pinnick, karo na biyu a shugabancin hukumar kwallon kafa ta tarayyar Najeriya (NFF) kuma shine ya zama mutum na farko da ya fara zarcewa a tarihin wannan kujera.

Amaju Pinnick ya doke abokan hamayyarsa wadanda suka hada da tsohon shugaban hukumar Alh Aminu Maigari, da Taiwo Ogunjobi wadda ya taba rike sakataran NFF da kuma Chinedu Okoye.

Pinnick, mataimakine na shugaban hukumar kula da kwallon kafa ta Afirka, ya samu nasarar ne da ga garumin rinjaye inda ya samu kuri'u 34 a cikin 44 da aka jefa tun a zagayen farko na zaben.

Ku Duba Wannan Ma Hukumar NFF Ta Yiwa Golden Eaglets Alkawri Idan Suka Doke Ghana

Aminu Maigari, ya na binsa da kuri'u 8 sai Ogunjobi wanda ya samu kuri'u, 2 rak shi kuma. Chinedu Okoye. bai samu koda guda daya ba.

Ga cikekken jerin sunayen shuwagabannin wadanda aka zabe su a ranar Alhamis a jihar Katsina.

1. Amaju Pinnick – Shugaba

2. Seyi Akinwnumi – Mataimakin shugaba na daya

3 .Shehu Dikko – Mataimaki na biyu

4. Ibrahim Musa Gusau – Mamba

5. Ahmed Yusuf Fresh – Mamba

6 .Felix Anyansi-Agwu – Mamba

7. Suleiman Yahaya-Kwande – Mamba

8. Babagana Kalli – Mamba

9. Sharif Rabiu Inuwa – Mamba

10. Chidi Ofo Okenwa – Mamba

11. Aisha Falode – Mamba.

Sauran kwamintin da ka zaban sun hada da

12. Mohammed Alkali – a.matsayin Mamba

13. Musa Duhu – Mamba

14. Ganiyu Majekodunmi – Mamba

15. Emmanuel Ibah – Mamba

sai kuma sakataren da zaiyi aiki dasu shine

16. Mohammed Sanusi –

Wadannan sune wadanda zasu ja ragamar hukumar tun daga shekarar 2018 zuwa 2022.

Zaben ya gudana ne a Jihar Katsina tare da wakilin hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA da na Afirka CAF.

Your browser doesn’t support HTML5

Amaju Pinnick Ya Yi Nasa Da Gagarumin Rinjaye