Al'ummomin Bajoga Sun Zargi Kamfanin Simintin Ashaka

Ma'aikacin kiwon lafiya

Al'ummomin Bajoga a karamar hukumar Bonakaye dake jihar Gombe sun zargi kamfanin simitin Ashaka da fitarda kura mai illa ga rayuwarsu.
Al'ummomin Bajoga dake cikin karamar hukumar Bonakaye a jihar Gombe sun zargi kamfanin siminti na Ashaka da fitar da kurar dake cusa rayuwarsu cikin wani mummuna hatsari na kamuwa da cututtuka.

Alhaji Hassan Mohammed shi ne kakakin al'ummar. Ya zanta da wakilin Muryar Amurka Abdulwahab Mohammed inda ya ce basa samun kyakyawar kulawa daga kamfanin a cikin fiye da shekaru talatin da ya yi yana gudanar da ayyukansa a kasarsu. Ya ce kamata ya yi kamfanin ya taimaka da samun hanyoyi da ruwan sha da asibiti kodayake yanzu ya taimaka da magungunan warkar da tari da asma ga wadanda suka kamu da su sanadiyar kurar siminti. Ya ce to amma yakamata kamfanin ya samarda asibitin da zai warkar da wasu cututtukan da mutane suka kamu da su sabili da shakar gurbatacciyar iskar. Kodayeke kamfanin na ba yaran ma'aikata ilimi kyauta, kakakin ya ce wannan ba shi da anfani idan shirin kamfanin domin 'ya'yan su maye gurbin iyayensu ne idan sun kamu da cutar da iskar ta jawo masu.

Yayin da yake mayarda martani game da zargin shugaban kamfanin Alhaji Umaru Kwairanga Sarkin Fulanin Gombe cewa ya yi wannan batun da al'ummar ke yi tsohon labari ne. Ya ce kamfanin a yanzu yana cikin kamfanonin duniya da suka daina fitar da kura mai illa. Ya ce yanzu komi ya canza. Ya ce da can da ka iso Gombe zaka ga kurar na tashi. Yanzu har mutum ya iso Ashaka ba zai ga kurar ba. Ya kara da cewa kwana kwanan nan kamfanin ya gina asibitin yara a Ashaka. A Gombe ma ya gina wurin kula da masu ciwon sukari. Bugu da kari mazauna kauyukan dake kewaye da kamfanin na zuwa shan magani kyauta a asibitin ma'aikatansu. Kana kurar da kamfanin ke fitarwa yanzu bata taka kara ta karya ba.

Abdulwahab Mohammed nada rahoto.

Your browser doesn’t support HTML5

Al'ummomin Bajoga Sun Zargi Kamfanin Simintin Ashaka - 3:27