A cewar Hajiya Mailafiya gwamnatin Najeriya ta himmatu wurin wayar da al'ummar kasar game da tsaftace muhalli domin rashin tsafta babban hanyar jawo ma kanmu cuturtuka ne. Hajiya Mailafiya ta yi misali da irin yadda ake kazanta a wurin yi da sayar da abinci da aka fi sani da suna mama put. Ta ce kwanukan da aka ci tuwo ko shinkafa haka za'a hadasu a wankesu cikin ruwa daya kana a zubar da ruwan kusa da inda mutane ke cin abincin. Ta ce to iskar muna shakanta tana iya kuma zama mana illa. Haka ma mutane na yin fitsari da kashi duk mu shaki iskarsu. Yin hakan ya kan yi sanadiyar wasu cututuka da muke fama da su.
Shugaban kulawa da muhalli na Jihar Neja Dr Yakubu Tanko ya ce suna murna da ranar domin irin matakan da jihar Neja ta dauka game da tsaftace muhalli. Ya ce kwana kwanan nan jihar ta dauki sabbin dubagari su dari biyar domin tabbatar da aiwatar da dokar tsaftace muhalli da gwamnatin ta kafa. Shi ma gwamnan jihar Dr Babangida Aliyu yayin da yake jawabi ya ce mako mai zuwa za'a kafa kotuna na musamman da zasu saurari kararraki da za'a rika kawo masu idan mutane sun karya dokar tsaftace muhalli.
Mustafa Nasiru Batsari nada rahoto.