Kwana guda bayan da kwamitin ya bada sanarwar dage zabukan kananan hukumomi al'ummar kasar sun fara mayar da martani akan lamarin.
Malam Yakuba Dan Iya wani mai nazari akan lamuran siyasa a kasar yace matakin da kwamitin ya dauka yayi daidai idana aka yi la'akari da zaben da aka yi saboda kowace kasa tana son a ce zabukanta sun yi daidai sun kuma zama abun koyi. Yake haka ma kowace tafiya tana da gyaran da za'a yi mata. Idan an yi tafiya irin ta da to ba za'a daina tsegumi ba.
Wasu 'yan kasar sun ce akwai abun da gwamnai ta gani har tace ta dage zaben. Wani ma yace zacen dage zabuka ba laifi ba ne tunda basa yiwuwa sai da kudi. Dole a yi hakuri tare da bin doka. Saidai kuma zancen da gwamnati ke yi na cewa 'yan hukumar zabe nada tabo to ai da ba'a bari sun gudanar da zabukan baya ba.
Abun jira agani ayanzu shi ne matakin da gwamnatin kasar Nijar zata dauka akan kansiloli da shugabannin hukumomin da wa'adinsu ya zo karshe.
Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5