Kusan shekaru biyu da suka gabata jihar Flato ta sami kwanciyar hankali idan aka kwatanta da wasu shekaru a baya. Amma a cikin ‘yan kwanakin nan wasu sassan jihar sun sami kansu cikin tashin hankali wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane fiye da arba’in a cikin wata daya.
Matasan jihar sun bayyana ra’ayoyinsu akan yadda suke gani za a fitowa lamarin.
A wata hira da yayi da wakiliyar sashen Hausa Zainab Babaji, Murtala Abdullahi ya fadi cewa akwai bukatar matasa su hada kansu kuma su nemi sana’ar yi don taimakawa kansu. Murtala ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni da su taimakawa matasa.
Shi kuma Mr. Sunday Adikitoyi, yace harkar kasuwanci, noma, siyasa da sauransu baza su yiwu ba in ba tare da zaman lafiya ba. Ya kuma yi kira akan a kawas da bambance-bancen da suka kawo rashin zaman lafiya don samun cigaba.
Ko ranar Talatar da ta gabata an yi rikici a wani yankin karamar hukumar Riyom dake jihar wanda yayi sanadiyar hallaka mutane uku, wasu mutane biyu kuma na kwance asibiti ana yi masu jinya.
Ga karin bayani a cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5