Al'umar jahar Barno, sun bi sawun takwarorinsu da dama a aarewacin Najeriy wajen bayyan afarin cikin samun labarin cewa shugaba Muhammadu Buhari yace za'a sake karawa dashi a zaben kasa mai zuwa idan Allaha Ya kai mu.
Wannan ya biyo bayan sanarwar da shi shugaban kasan da kansa ya yi a taron kwamitin gudanarwa a helkwatar jam'iyyar ake Abuja. Kamar yadda wakilin Sashen Hausa Haruna Dauda ya aiko mana;mutane yankin sun kagara da jin wannan labari.
Tun can baya uwar jam'iyyar APC da wasu jigajiganta na ta buga kirjin cewa basu da wani dan takara da ya wuce Shugaba Buhari. Dalili ke nan da wasunsu suke kai goro-su-kai-mari domin tabbatar da cewa shugaban ya sake tsayawa. Da ma su jam'iyyun adawa na barazanar cewa zasu kwace mulki daga jam'iyyar APC shekara mai zuwa.
A Maiduguri jama'a na tofa albarkacin bakinsu akan yunkurin sake tsayawa zabe da shugaban ya yi. Husseni Abba Kyari yace suna murna da abun da baba Buhari ya fada, da fatan Allah ya tabbatar da alherinsa saboda shekaru ba zasu hana mulki ba..
Mustapha Muhammad yace ya yi murna sosai da jin cewa Shugaba Buhari zai sake tsayawa. Injishi idan shugaban mai ci gaba da mulki ba aikinsa na baya zai wargaje. Shi ma Hassan ya tsaya a shekarar 2019 saboda ya samu ya yi aiki da kasafin kudin da ya yi.
Muhammad Awal ya taya jama'a murna ne da jin labarin cewa Shugaba Buhari zai sake tsayawa takara yana cewa abu ne mai alheri.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5