Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Me 'Yan Najeriya Ke Cewa Dangane Da Takarar Buhari a 2019?


Shugaban Najeriya yayin kaddamar da tashar tekun kan tudu
Shugaban Najeriya yayin kaddamar da tashar tekun kan tudu

'Yan Najeriya na ta bayyana ra'ayinsu dangane da sanarwar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi na sake tsayawa takara a zaben 2019, lamarin da yake shan yabo da suka.

Bayan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana sha’awarsa ta neman yin wa’adi na biyu a zaben 2019, wasu ‘yan Najeriya musamman a shafukan sada zumunta, na ta bayyana ra’ayinsu dangane da matsayar shugaban.

Yayin da wasu ke yin na’am da matsayar ta Buhari wasu kuwa akasin hakan suke ta bayyanawa.

Mun leka shafin Facebook na Sashen Hausa na Muryar Amurka inda muka tsakuro kadan daga cikin ra’ayoyin da masu bibiyan shafin suka bayyana kan labaran da muka wallafa dangane da aniyar da shugaba Buhari ya bayyana.

Wani mai bibiyan shafinmu na Facebook mai suna Nura Muhammad cewa ya yi “Wallahi ba na sanka, don girman Allah da Annabi ka yi hakuri haka ya isa.”

Sai dai a nashi tsokacin, Bello Ahmed Dasin cewa ya yi “Allah ka bashi ikon sake tsayawa. Baba Buhari sai ka yi da ikon Allah,” kamar yadda Dauda Musa Barigima Dandume ya yi na’am da labarin, inda ya ce “hakika mu ‘yan Najeriya muna goyon bayan baba Buhari dari bisa dari domin kara neman shugabanchin kasar nan a karo na biyu kuma muna fatan alkairi.”

Ita ma Hauwa'u Ibrahim cewa ta yi “Masha'ALLAH.....ALLAH ya ba shi Nasara, lafiya, 'kwarin gwiwa da juriyar rike kasa ta Nigeria.”

Amma Usman A. Usman Kirfi ana shi tsokacin cewa ya yi, “akwai ayar tambaya a wannan magana ta shi, sama da shekaru 3 talakawa suna kuka kuma kana gani ba ka yi komai ba sai a zabe na gaba ne za ka yi?

Shi kuwa Dauda Idriss Dan Karai-karai cewa ya yi “Alhamdu Lillah Hakika mu talakawan Nageriya muna murna da maraba da sake tsayawan Shugaban Nageriya Muh'd Buhari takaran Shugaban kasa karo na biyu karkashin Jam'iyar APC ALLAHU Ya kai mu 4+4=8 Inasha Allahu.”

Kamar wadanda suka soki lamarin, shi ma Ibraheem Yahuza cewa ya yi, “indai kiran talakawa ne to baba ka yi hakuri, mu dai ba mu kira ka ba, kadai fito dan radin kanka ne, me jiya ta yi balle gobe in an yi magana a ce wai na kewaye da shi ne suka hana shi aiki to yanzun ma ai tare za su koma.”

A dai yau Litinin shugaban na Najeriya, ya bayyana shirinsa na sake tsayawa takara a zaben 2019, a lokacin wani taron shugabannin jam’iyyarsa ta APC a Abuja.

Mai bai wa shugaban shawara a fannin sabbin kafafen yada labarai, Alhaji Bashir Ahmad ne ya ce Buhari ya ce zai nemi wa’adi na biyu ne bayan da ya yi la’akkari da “kiraye-kirayen” da jama’a ke yi na ya sake tsayawa takara.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG