Al'umma Ta Shagala Da Dabi'un Girmamawa Da Kyautatawa- Inji Kicima

Hamza Kicima

Hamza Kicima mawaki ne wanda ya fi maida hankali ga fannin fadakarwa da wakokin da suka danganci siyasa ya ce ya fi mai da hankalinsa ne ga bangaren fadakarwa duba da yadda al’umma suka shagala a yanzu ta inda aka bar dabi’un girma zuwa na karanta da rashin kyautatawa.

Kicima ya ce a mafi yawan lokuta wakokinsa na duba matsalolin da ake fuskanta a yanzu inda ya bada misali da wata wakarsa da ya rera wadda ke nuni da gajen hakuri na al'umma inda da zarar wani ibtila’I ya afku ga dan adam sai ya alakanta hakan da wani na sa ta hanyar cewar an tsafface shi.

Kicima ya ce yawan shiga bokaye da masu aikata tsafi ya yawaita , har ila yau ya ce yana wakokin da suka danganci auren zamani inda ya ce mata a yanzu basa aure sai da niyyar samun mai kudi domin ko da bayan aure zasu samu gado mai soka, koda shike haka lamarin yake ko a bangaren maza.

Hamza ya ce ire-iren wadannan matsaloli ne yake dubawa a wakokinsa ,kuma ya fi maida hankali tare gudanar da wakokinsu a kan wadannan matsaloli na yau da kullum da niyyar za’a fadakar da al’umma sannin ire-iren wadannan matsalolin da ke faruwa a yanzu.

Daga karshe ya kara da cewar daga cikin kalubalen da yake fuskanta shine yadda wasu daga cikin mawakan ke kushe wakokin ‘yan uwansu mawaka.

Your browser doesn’t support HTML5

Al'umma Ta Shagala Da Dabi'un Girmamawa Da Kyautatawa- Inji Kicima