Karamar hukumar kuje a shake da jama’a masamman ma’aikata dake aiki cikin babban birnin taraiya kuma garin na daf da babban filin jirgin Karamar saman Abuja.
Firgita dai da Ebola, da yanda Ebola ke kashe mutane, bai rasa nasaba da yanda mazuana Kuje da shugaban karamar hukumar Shaban Tete, suka ce sam ba zasu amince da kafa cibiyar kula da masu Ebola, a babban Asibitin garin ba.
Wannan bijirewa bata yima Ministan Abuja, Bala Muhammmad, dadi ba sai dai da alamu barazanar tayi sauki, Rilwanu Muhammad, shine babban sakataren hukumar lafiya matakin farko na Abuja, yace yana fata jama’a zasu gane cewar da cutar na bin iska ‘yan Amurka, da suka kamu da cutar da ba’a kaisu Amurka ba.
Har dai fatan da akeyi cewa cutar ta tsaya ne a Legas, kuma bata bazu a sauran sassan Najeriya ba kamar yanda Minista, a ma’aikatan lafiya, Haliru Alhassan, ke bayani ba mamaki ma ko an kafa cibiyar bazata samu ajiyar majinyata ba.
Alumar Kuje dai sunyi zarwance in dai don kusanci da jama’a ne mai zai hana a kafa cibiyar a babban asibirtin Abuja ba wanda ke cikin gari maimakon tafiya nesa har zuwa Kuje.
Your browser doesn’t support HTML5