Al'umar Fulani da Sayawa na karamar hukumar Tafawa Balewa da ke jahar Bauchi sun yi wani buki domin nuna wa Duniya farin cikin su na dawo da zaman lafiya a tsakanin al'umomin biyu da suka kwashe shekaru da dama suna zaman doya da manja wanda ya jawo rasa daruruwan rayukan jama'a.
Sarakunan Fulani da na Sayawan dai sun yi bayanai da dama a lokacin taron. Mr Joseph Sale shugaban al'umar sayawa yayi karin bayanin cewa, sun kira wannan taro ne domin su nuna wa duniya cewar al'umar Sayawa da Fulani sun kudiri aniyar zaman lafiya tsakanin su.
Shugaban ya kara da cewa sanadiyyar kiran wannan taron ya samo asali ne daga mutane biyu, wato Honourable Yakubu Dogara na majalisar taraiya da kuma Alhaji Tukur daga yankin Fulani wadanda suka hada hannu wajan kira da janyo hankalin sauran 'yan Uwan su daga dukkan bangarorin da cewar lokaci yayi da yakamata su rungumi juna domin zaman lafiya a daukacin jahar.
Shima shugaban Fulanin mai suna Jauro Baidu dan shekaru tamanin da daya cewa yayi bazai taba mantawa da wannan rana ba domin irin mahimmancin ta a gare su, dalili kuwa a cewar sa, a wannan gari aka haifi iyayen sa. ya kuma nuna matukar farincikin sa tare da godiya ga wadan da suka tsaya tsayin daka domin ganin yiwuwar wannan taron.
Matasa daga dukkan bangarorin sun tofa albarkacin bakin su da kuma farin ciikin wannan tarayya tsakanin su da abokan zaman nasu.
Ga Abdulwahab Mohammed da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5