Ilimi ginshikin rayuwar dan Adam,ne, wata ma’aikaciyar lafiya Mariya Yahya Wudil, ce ta bayyana hakan yayin da take zantawa da Baraka Bashir, wakiliyar DandalinVOA a birnin kano.
Malama Mariya ta ce burinta ya cika tunda ta cimma dukkanin muradan ta na rayuwa sakamakon ilimin bokon da iyayenta da maigidanta suka mara mata baya akai.
Ta kara da cewar bayan kamala makarantar sakandare a Kachako, take da muradin son ta zama malamar asibiti, kuma hakkarta ta cimma ruwa domin bayan yimata aure ta kuma haifu mai gidanta ya bata damar zuwa makaranta domin cika mata burinta na rayuwa.
Ta sami damar shiga makarantar Clinical assistant a Birnin Kudu a matakin farko na zama malamar asibiti. daga bisani ta samu gurbin karatu a makarantar school of Hygine dake garin Kano, inda ta kamala diplomarta a fannin Environmetal health, wanda ya bata zama jami’ar lafiya.
Ko dayake malama Mariya ta ce tun da ta fara karatu har kammalawa kawo yanzu da ta yi shekaru ashiri (20) tana aiki bata taba fuskantar wata matsalar da ya fi karfinta ba.
Your browser doesn’t support HTML5