Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta fada jiya Litinin cewa hare haren ta’addanci da tashe-tashen hankula a Iraki sun kashe akalla fararen hula 6,878 tare da raunata wasu 12,388 cikin shekarar da ta gabata.
WASHINGTON, DC —
Amma ta yiwu ainihin adadin wadanda rikicin ya shafa ya fi haka, saboda ba a hada da fararen hula da aka kashe ko suka jikkata a Lardin Anbar dake yammacin Iraki a cikin watannin Mayu, da Yuli da Agusta, da kuma Disamba ba.
Za a iya cewa wannan shine tabbataccen adadi, a cewar shirin ba da agaji na MDD a Iraki da ake kira UNAMI a takaice.
MDD ta kuma fadi cewa adadin fararen hular da rikicin ya shafa a watan Disamba bai kai na watannin da suka gabata ba, duk da karin harin boma boman da ‘yan ta’adda suka kai zuwa karshen watan, wanda suka auna fararen hula.