Sabon shugaban kasar Malawi, Lazarus Chakwera, ya karbi rantsuwar kama aiki a babban birnin kasar, Lilongwe, biyo bayan nasarar da ya samu zagayen zaben na biyu da aka yi a ranar 23 ga watan Yuni.
Yayin bikin rantsuwar kama aikin, a jiya Litinin, Chakwera ya yi alkawarin gabatar da wasu sauye-sauye don magance matsalolin cin hanci da rashawa da kuma samar da abinci a kasar da ta ke kudancin Afirka.
Bikin rantsuwar da farko an shirya shi ne ya tafi da bikin ranar samun ‘yancin kan kasar a filin wasa na kasa da kasa na Bingu mai daukan mutum dubu 40,000.
Amma Chakwera ya soke bikin ranar samun ‘yan cin kan kasar jiya Lahadi yayin da ake daukan matakan dakile karin adadin wadanda suke da COVID-19.
A cikin wani jawabi da ya yi wa kasa, Chakwera ya sanar da matakai da dama na ciyar da kasar gaba, wanda ya ce ta shafe shekara 26 tana fama da matsalar rashin shugabanci na gari a lokacin da jam’iyyarsa ke bangaren adawa
Amma wasu ‘yan Malawi sun ce sun sha jin irin wadannan alkawuran a baya.