Ba za’a yada hotunan gasar firimiyar da kyamarar alkalin wasan zata nada kai tsaye ba, saidai za’a yi amfani da shi a matsayin wani bangare na shirin da za’a haska nan gaba a cikin shekarar da muke ciki da nufin “bada haske tare da ilmantarwa game da bukatun alkalancin wasa” a babbar gasar kwallon kafar ingila.
Gillett zai daura na’ura akansa wacce zata zamo cikin na’urorin sadarwar da alkalan wasa zasu rika daurawa a manyan wasannin kwallon kafa.
Kyamarar wacce wa’adin aikinta baya wuce sau daya ta samu amincewar hukumomin dake tsara dokokin wasanni da Hukumar Kula da Kungiyoyin Kwallon Kafa na Duniya (IFAB) da Hukumar Shirya Gasar Firimiya da Kungiyar Kwarrarun Alkalan Wasa mai Zaman Kanta da kuma Kungiyoyin Kwallon Kafar da abin ya shafa.
Sanarwar da Hukumar Shirya Gasar Firimiyar ta fitar tace, “muna mika godiya ga kungiyoyin kwallon kafar Crystal Palace da Manchester saboda goyon bayan da suke baiwa wannan tsari.”