Alkalin Kotun Kolin Amurka Ruth Bader Ta Rasu

Ruth Bader Ginsburg

Alkali Ruth Ginsburg wadda ta dade a matsayin alkalin kotun Amurka ta rasu yau jumma'a bayan ta yi fama da rashin lafiya na tsawon lokaci.

Ruth Bader Ginsburg wadda ta yi kaurin suna a batun kare hakkin mata da yaki da nunawa mata wariya, kuma daya daga cikin alkalan kotun koli da ake mutuntawa ta rasu ne bayan ta yi fama da ciwon sankara.

Sanarwar da kotun koli ta fitar ta bayyana cewa, Ginsburg, mai sassaucin ra'ayi kuma mace ta biyu da aka zaba a matsayin alkalin kotun koli, ta rasu ne a gidanta tana da shekaru tamanin da bakwai a duniya.

A cikin sanarwar, alkali John Roberts ya bayyana cewa “kasarmu ta yi rashin alkali mai cike da tarihi."

Ginsburg ta fara taka rawar gani wajen kare 'yancin mata da kuma hakkokinsu a Kotun Kolin tun shekara ta 1993.