Sai dai kuma nan take kotu ta bayar da belin su, bisa ka’idar mai tsaya musu ya zamanto yana da gida a unguwar masu kudi dake Sokoro ko Maitama.
Rashin samar da mai tsaya musu kan wannan shari’a ta zargin yin dokokin majalisa na jabu zai sa a turasu gidan Yari dake Kuje.
Joseph Daudu shine lawyan dake kare Bukola Saraki, yace sun roki kotu a jawabinsu da lawyoyi suka saba yi kuma kotu ta amince ta bayar da belinsu. A nasa bangaren lawyan dake kare gwamnati Muhammad Sa’idu ya dage kan kar a baiwa su Bukola beli, amma hakan bai samu karbuwa ba.
Alkalin yace ya bada belin Bukola Saraki da mataimakinsa saboda ba a riga an samesu da laifi ba, kuma wadannan mutane da gwamnatin tarayya ta shigar da kara a kansu suna da kima a idanun duniya, domin mukaman da suke rike da su.
Dinbin magoya bayan Bukola saraki sunyi dafifi a kotun, kotun dai ta dage sauraron karan har zuwa sha ‘daya ga watan Yuli mai zuwa.
Saurari rahotan Madina Dauda.
Your browser doesn’t support HTML5