Alkalan Nijar Na Yajin Aiki

Nijar

Alkalai a Jamhuriyar Nijar, sun fara yajin aikin kwanaki biyu daga yau Alhamis, da nufin nuna rashin amincewa da wani kwaskwarima da gwamnatin kasar ke shirin yi wa tsarin daukar alkalan aiki.

Sun bayyana cewa matakin na barazana ga aikin alkalanci da ma fannin shara’a baki daya.

Kudirin dokar da tuni Majalisar dokokin kasar ta yi na’am da shi, zai takaita hanyoyin shiga aikin alkalanci a jamhuriyar Nijar.

Matakin da kungiyar alkalai ta SAMAN ta ce ba za ta laminta da shi ba, ‘shi ne mafarin wannan yajin aiki’, inji mai shara’a Zakari Yaou Mahamadou.

Your browser doesn’t support HTML5

Alkalan Nijar Na Yajin Aiki

Kungiyar SAMAN, ta jingine aiki daga yau Alhamis har zuwa gobe Juma’a, da nufin nunawa shugaban kasa rashin cancantar kudirin da yake shirin sakawa hannu.

Da wakilin Muryar Amurka ya tuntubi ministan shara’a ta waya domin jin matsayin gwamnati akan wannan badakala, bai amsa ba.

AI’umma, a nasu bangare, sun fara korafi akan illolin wannan yajin aiki yayinda wani mazaunin gari, Mounkaila Soumaila, yace yau alkali ke nemansa saboda shara’ar dake tsakaninsa da wani, kuma ya bar aikin dake gabansa saboda wannan shari’a, amma ya tarar ana yajin aiki.

Yace gaskiya bai ji dadin haka ba, saboda haka suna fatan za’a sasanta domin idan aka ci gaba a haka, talakkawa a kansu abin zai kare.

Yajin aikin dake gudana a daukacin kotunan jihohi 8 na Nijar, ya samu karbuwa a wajen alkalai magoya bayan SAMAN, inji shugabanin wannan kungiya, saboda haka Sakatarenta mai shara’a Nouhou Aboubakar na baiwa jama’a hakuri.

Saurari rahoto cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Alkalan Nijar Na Yajin Aiki