Alkalai a kotun Kenya sun ba da dalilai da dama kan hukuncin da suka yanke a ranar Alhamis, inda Alkali Antony Mrima ya karanta wani bangare na hukuncin domin bayyana dalilin da ya sa suke bari sabon mataimakin shugaban kasa na gabashin Afrika ya shiga ofis.
"Ra’ayin jama’a game da wannan al’amarin ya fi karkata ga abin da kundin tsarin mulki ya tanada, wanda a kowane hali yana wakiltar muradin jama’a." In ji Alkali Mrima
Tun a farkon watan Oktoba, Majalisar Dattawan Kenya ta zabi ci gaba da tuhumar tsohon mataimakin shugaban kasa Rigathi Gachagua kan laifuka biyar daga cikin guda 11 da ake zarginsa da su, ciki har da take dokokin kasa da kuma zarge-zargen cin hanci da ya ce an shirya don a bata masa suna.
Shugaba William Ruto ya zabi Ministan Harkokin Cikin Gida, Kithure Kindiki, domin maye gurbin Gachagua, wanda lauyoyinsa suka kalubalanci wannan zabin.
Kotun Koli ta dakatar da daukan duk wani mataki har sai ta kammala saurarar ra'ayoyin bangarorin biyu.