Alkalai a jihar Neja sun yi barazanar tafiya yajin aiki idan har gwamnatin jihar ta ki biyansu wasu hakokinsu cikin kwanaki ishirin masu zuwa.
Alkalan sun zargi gwamnatin jihar da mayar dasu saniyar ware wajen biyansu wasu alawus alawus da kuma samar masu da kayan aiki a kotunansu musamman kotunan majistaret da na shari'a. A cewar alakalan an jefasu cikin mawuyacin hali.
A cikin wata wasika mai shafi biyar da alkalan suka aikawa gwamnatin jihar sun nuna damuwa akan halin da suka ce sun shiga na rashin kulawa dasu kamar yadda yakamata. Sun ba da misali da wani alakalin da wasu 'yan bindiga suka yi garkuwa dashi kwanakin baya.
Mai shari'a Sa'adatu Abubakar Gambo ita ce mai magana da yawun kungiyar alkalan. Injita suna da koke koke da yawa da yanzu suka fi karfinsu. Misali, wani alkalin da aka sace ya fito daga aiki ne yana takawa zuwa gidansa saboda bashi da motar hawa. Akan hanya aka saceshi. Alkalin ya yi wajen shekaru 20 yana aiki. Ta kara da cewa gwamnati bata sayawa alkalan kotuna motoci ba. Injita su ne suke aiki a karkara kuma masu aikata laifuka sun fi sanin alkalan majistaret da manyan alkalai.
Kwamishanan Shari'a na jihar Barrister Nasara Dan Malam ya shaidawa Muryar Amurka cewa bai ga wasikar alkalan ba saboda baya gari ya yi tafiya.
Sai dai wani lauya mai zaman kansa ya ce tabbas alkalan na da hurumin bin hakkinsu amma matakin zuwa yajin aiki ya na da tsanani.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5