Alkalan sun mikawa sakataren hukumar wasikarsu ta janyewa daga hukumar domin amsa kiran kungiyar tasu.
Kungiyar alkalan kasar wacce mataimakin sakatarenta Nuhu Abubakar yace sun dade suna yiwa gwamnati hannunka mai sanda saboda zargin shigshigi a sha'anin shari'a. Yace sun zauna sun tattauna dasu amma suka ce akwai matsaloli. Sun kira gwamnati ta gyara matsalolin to amma, wai ba'a sauraresu ba
Nuhu Abubakar yace lamarin ya baci har ya kaiga barin alkalai wajen ishirin da ba'a basu wurin aiki ba ba'a kuma koresu daga aiki ba. Yace an ki basu wani aikin da zasu yi. Ba'a kuma basu wani dalili ba ko gaya masu laifin da suka yi da ya sabawa ka'ida.
Kungiyar alkalan tace ta dauki wannan matakin ne domin ba gwamnatin Nijar daman gyara kuskuren da ta tafka.
Jami'in hulda da jama'a a ma'aikatar shari'a yace ministan shari'a na shirin rubutawa kungiyar alkalan amsa.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5