Aliko Dangote Da Abdulsamad Rabiu Sun Yi Asarar Dala Biliyan 5.85 Sakamakon Sake Naira

Aliko Dangote

A wani al'amari na baya-bayan nan, fitattun attajirai biyu na Najeriya, Aliko Dangote da Abdulsamad Rabiu, sun yi asarar dala biliyan 5.85 baki daya, kamar yadda cibiyar Bloomberg Billionaire Index (BBI) ta bayyana.

Wannan asarar dai ta faru ne jim kadan bayan da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bijiro da wasu canje canje akan kudin kasar, lamarin da ya haifar da sauye-sauye a kasuwannin canji.

Bloomberg Billionaire Index (BBI) shafi ne wanda ke matsayin kima na yau da kullun na mutane mafiya arziki a duniya, ya na fitar da bayanai sahihai masu mahimmanci game da ƙididdigar ƙimar kowane hamshakin attajirin duniya.

Ya zuwa ranar 15 ga Yuni, 2023, bayanai daga (BBI) sun nuna asarar da manyan attajiran na Najeriya suka fuskanta a kasuwancinsu na yau da kullum.

Aliko Dangote, wanda shine mafi arzikin mutum bakin fata a duniya kuma mafi arziki a duk nahiyar Afirka, Shugaban Kamfanin Dangote kuma Shugaban Rukunin Dangote, ya yi asarar kusan dala biliyan 3.12 a sabon sake fasalin da aka yi a tsarin kudin naira da ya faru a baya bayan nan.

Hakazalika, Abdulsamad Rabiu, shugaban kamfanin BUA Group, ya samu raguwar dala biliyan 2.73 a dukiyarsa.

Shugaban Kamfanin Simintin BUA, Abdul Samad Rabiu.

An samu asarar ce a cikin kwana daya da matakin da babban bankin kasar CBN ya dauka na sauye sauye da bai wa bankunan kasar damar cinikayyar farashin dala a kasuwar canji ta bai daya.

Za ta iya yiwuwa kila tashin farashin Naira na baya-bayan nan ya haifar da sauyin yanayi a kasuwannin canji, lamarin da ya janyo koma bayan kudi ga wadannan attajirai.

Karkashin sabon tsarin kudin, ana kayyade darajar Naira ne ta hanyar karfin samar da bukatu a kasuwar canji. Hakan na nufin ba za a sake samun tsayuwar farashin canji na cinikin kudaden waje a Najeriya ba. Don haka, an kawar da shigar da CBN kai tsaye a kasuwar canji.

Kamar yadda bayanai daga FMDQ OTC Securities Exchange suka nuna, Naira ta rufe a kan N664/dala a ranar Laraba a kasuwar masu saka hannun jari da masu fitar da kayayyaki (I&E) bayan ta tashi tsakanin N700 zuwa N755 zuwa Dalar Amurka.

Faduwar darajar Naira

Tagar masu saka hannun jari da masu fitar da kaya (I&E) na aiki a zaman dandalin ciniki na musayar kuɗi a hukumance a Najeriya. Na ba da kasuwa ga masu zuba jari, masu fitar da kayayyaki, da masu kasuwanci don cinikin kuɗin waje a farashin musaya da aka ƙayyade ta yanayin kasuwa.

Duk da cewa ba a fayyace takamammen dalilan da suka haddasa asarar ’yan kasuwar ba, manazarta na nuni da cewa sauye-sauyen da aka samu a kasuwannin canjin kudade da ake samu a dalilin tashin Nairar ya taka rawa wajen takurewar arzikinsu.

Yayin da yanayin kasuwancin Najeriya ke ci gaba da daidaitawa da sabon tsarin musayar kudaden waje, mahalarta kasuwar, ciki har da hamshakan attajirai kamar Dangote da Rabiu, za su bukaci yin la'akari da yanayin tattalin arzikin da ke tasowa don rage hadarin hada-hadar kudi da kuma cin gajiyar damarmaki masu tasowa.

~ Yusuf Aminu