Alhazai kimanin dubu uku ne daga Ghana suka gudanar da hajjin bana, kuma kamar yadda hukumar tace, mutane biyu sun rasu kuma mace daya ta haihu a kasa mai tsarkin.
Mataimakiyar babban jami’in sadarwar hukumar hajji ta Ghana, Hajiya Mariam Sissy, ta shaidawa Muryar Amurka cewa, an kammala duk shirye-shiryen da ya kamata, kuma tawagar farko da suka tashi daga filin tashi da saukar jiragen sama na Tamale ne za su fara zuwa, sannan ranar 23 ga wata, tawagar Accra za su fara tashi sai a kammala gaba daya a 28 ga wata.
Yana daga cikin dokar kasar Saudiyya cewa duk alhazai su isa filin jirgin sama awanni takwas kafin su tashi, Hajiya Mariam ta bayyana cewa, hukumar za ta tabbatar cewa kowa ya samu abinci yayin da suke jiran tashinsu zuwa gida sannan kuma kowa zai sauka da jakukkunansu a Ghana.
Hajiya Maryam ta tabbatar da cewa duk wadanda ba su samu tafiya ba, bayan kwanaki biyar da kammala jigilar alhazan zuwa gida, za a biya su kudadensu
Wasu alhazan sun bayyanawa Muryar Amurka cewa ba su samu matsala a hajjin bana ba.
Alhazan Ghana na bana, sun tashi zuwa Saudi Arabiya, ranar 20 ga watan Yuni, 2022. Hakan na nufin cewa, sun yi wata daya cif-cif a kasa mai tsarki.
Sauarari cikakken rahoton Idriss Abdullah Bako cikin sauti :
Your browser doesn’t support HTML5