Alhasan Ado Doguwa Ya Lashe Zabe A Kano

Alhasan Ado Doguwa

Alhasan Ado Doguwa

Jimullar kuri’un da aka kada a wannan zabe da aka yi a ranar Asabar a mazabar ta kai 79,705, kuri’un da aka amince da su kuma 78,788 yayin da aka yi watsi da 917.

Shugaban masu rinjaye a Majalisar Wakilan Najeriya Alhassan Ado Doguwa ya lashe zaben da aka sake a mazabar Doguwa da Tudunwada da ke Kano.

Baturen zaben hukumar ta INEC Farfesa Sani Ibrahim ne ya ayyana Doguwa a matsayin wanda ya lashe zaben.

Doguwa na APC ya samu kuria’ 41, 573 yayin da babban abokin hamayyarsa Yusha’u Salisu na jam’iyyar NNPP ya samu kuri’a 34, 813 sai dan takarar PDP da ya samu kuri’a 211.

Jimullar kuri’un da aka kada a wannan zabe da aka yi a ranar Asabar a mazabar ta kai 79,705, kuri’un da aka amince da su kuma 78,788 yayin da aka yi watsi da 917.

A jihar Kano, zaben cike gurbi na 'yan majalisar dokokin jiha da na tarayya da aka yi ya shafi kananan hukumomi 15 daga cikin kananan hukumomi 44 na jihar. Sai dai an fuskanci karancin fitar masu kada kuri'a.