Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa INEC Ta Cire Alhassan Ado Doguwa Daga Jerin Sunayen Wadanda Suka Lashe Zabe


Alhassan Ado Doguwa (Facebook/ Naz Photography)
Alhassan Ado Doguwa (Facebook/ Naz Photography)

A ranar Larabar da ta gabata ne wata kotun Magistira a Kano ta tisa keyar shugaban masu rinjayen na majalisar tarayya zuwa gidan gyara hali.

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta cire sunan shugaban masu rinjaye a majalisar wakila wanda yake cikin wani rikici Alhassan Ado Doguwa daga jerin sunayen wakilan da suka yi nasara a zaben da ya gabata.

Wannan mataki na hukumar ya faru bayan da INEC ta ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu a mazabar Doguwa da Tudunwada.

A cewar baturen zabe na wannan mazaba, Farfesa Ibrahim Adamu Yakassai, dan takakarar na jam’iyya mai mulki APC wato Doguwa, ya yi galaba akan abokin hamayyarsa Yusha’u Salisu Abdullahi dan takarar jam’iyyar NNPP da kuri'a 39, 732.

Abduallahi kuma ya samu kuri'a 34, 798

Sai dai ya zuwa yanzu INEC ba ta saka sunayen a shafinta na twitter ba, kana, ta ce baturen zaben ya bayyana sakamakon domin an tursasa shi.

Kuma a dalilin kenan da ya sanya hukumar fidda sunan Dogiwa daga cikin wadanda suka yi nasara a zaben.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito a baya cewar Doguwa ya shiga hannun hukuma ne bisa zarginsa da ake yi masa na kisan wasu mutane tare da kona ofishin jam’iyyar NNPP a lokacin gunadar da zaben na watan jiya.

A ranar Larabar da ta gabata ne wata kotun Magistira a Kano ta tisa keyar shugaban masu rinjayen na majalisar tarayya zuwa gidan gyara halinka.

Sai dai kuma, rahotanni a ranar Litini na nuni da cewar wani mai shari’a Muhammad Inusa ya ba da belin wanda ake zargi da kisa da kuma kona wuri akan kudi naira miliyan dari biyar (500,000,000.)

Sannan an haramta masa zuwa mazabarsa a lokacin zabe mai zuwa na gwamna wanda za a gudanar a ranar Asabar mai zuwa 11 ga wannan wata mai ci Maris.

Mai shari’ar ya yi wa Doguwa umarnin kawo mutane biyu da zasu masa lamuni kuma wajibi daya ya kasance mai sarauta ya kasance mai daraja na farko da kuma babban jami’in gwamnati.

Mai shari’ar ya ba da belin bayan da lawyan wanda ake kara Nuraini Jimoh ya bayyana a kotu cewa, tuhuma kawai akeyi kuma duk wanda ake tuhuma, ana sa ran yana da gaskiya har sai an tabbatar da ya aikata laifin.

XS
SM
MD
LG