Yau ce ranar ma’aikata a Najeria, kuma an ware kusan Naira BIliyan uku da rabi domin sallamar shugaban kasa mai barin gado GoodLuck Ebele Jonathan da mataimakin sa da kuma sauran ‘yan majalisu da kuma masu rike da mukaman siyasa a matsayin kudaden sallama daga aiki bayan kasa samun nasarar zaben da ya gabata.
Bada sanarwar fitar da wadannan makudan kudade yazo daidai ne da lokacin da ma’aikatan Najeriya suka bi sahun sauran ma’aikata a kasashen duniya daban daban wajan gudanar da ranar ma’aikata.
Wasu daga cikin ma’aikatan sun koka da cewa kudaden da ake biyan ‘yan siyasar ta Najeriya ya fi na wasu sauran kasashen duniya da suka daurewa demokaradiyya gindi.
Fatan ma’aikan dai shine kawo karshen kashin dankalin da ake yi ma kananan ma’aikata da kuma sauran talakawa da ma cika alkawuran da gwamnati mai shudewa tayi masu. Da kuma fatan samun canji wurin sabuwar gwamnati mai jiran gado.
Your browser doesn’t support HTML5