Albashin malaman firamare bai taka kara ya karya ba - A.Y. Dabo

A wannan dakin karatu a wata makaranta an bar yara babu malami

A tsokacin da Malam Ysusf Abdullahi Dabo malamin kwalajin Abubakar Tatari Ali Polytechnic dake Bauchi ya yi yace albashin malaman firamare bai taka kara ya karya ba

Yace abun da aka yiwa malaman firamare ya tayar masa da hankali domin albashinsu bai taka kara ya karya ba kuma ba'a biyansu kan lokaci sai sun yi wata da watanni kafin a gutsura masu wani abu.

A jihar Bauchi an mayar da malami kusan juji ko bola saboda an dauka cewa sai mutum ya rasa aikin yi ne yake zuwa shiga aikin malunta ko kyaswa. Wannan ya sa ake nuna halin ko in kula ga malamai, musamman malaman firamare.

Dangane da matsalolin ilimi a jihar Bauchi yace abu ne da yakamata gwamnati ta yi wani hobasa wajen cetoshi a jihar. Musamman a duba ilimi daga makarantun firamare. Shi ne gimshiki. Idan ba'a samu a kafa tushe mai kyau ba ba za'a iya cigaba ba.

Ita wannan makarantar Sa'adu Zungur da ta kasance daya tilo dake da kujeru da kayan aiki ba domin talakawa gwamnatin da ta shude ta ginata ba. Wai wata makaranta ce zata zo gada kasar waje ta yi anfani da makarantar domin a sa 'ya'yan masu kudi da masu iko.Maganganun mutane ne suka tilastawa gwamnati barin makarantar wa talakawa.

Daga wannan makarantar Dabo yace kamata ya yi gwamnati ta dinga yin abu domin Allah da al'umma ba domin wasu dalilai daban ba. A cire son kai da kwadayi.

Yace duk lokacin da za'a sa ilimi ya zamo kamar siyasa to babu inda za'a je. A yanzu makarantun Bauchi ana iya cewa ba ma makarantu ba ne. A duba daga yadda ake diban malaman. Malaman yanzu basu da kwarewa domin kafin ma a dauki malami sai yana da gata. Malaman dake koyaswa a firamare yanzu su kansu suna bukatar ilimi bai kamata a ce suna koyaswa ba. Malaman firamare din basu da kwarewa saboda haka basa iya koyas da yara. Gwamnati bata duba cancantar malamai kafin ta daukesu aiki ba. Sai dai a ba mutum aiki domin iyayensa ko wani daurin gidi da yake dashi. Wannan abu na cikin dalilin tabarbarewar ilimi a jihar Bauchi

Ga cikakken bayani.