Tun daga Gombi har zuwa garin Mubi ana iya ganin irin barnar da 'yan Boko Haram suka yi a garuruwan da suka mamaye can baya.
Garurwan sun rasa rayuka da dama da dukiyoyi. Wasu kuma masu dimbin yawa sai da suka bar muhallansu domin su samu su tsira da rayukansu. Har yanzu ana tsintar gawarwaki a nan da can da fankon harsashai.
Jami'an tsaro tare da taimakon 'yan kato da gora da kungiyar maharban jihar Adamawa sun samu sun kwato garuruwan daga hannun 'yan Boko Haram. Kokarin nasu ya sa sun kwato garuruwa daga Gombi zuwa Maiha har Mubi.
Harkoki sun fara kankama a Maiha da Mubi da sauran garuruwan da aka kwato. A garin Mubi Muryar Amurka ta zagaya domin gani da ido.
Wadanda aka zanta dasu sun nuna farin ciki da godiya ga Allah da jami'an tsaro sabili da kwato garin Mubi. Yanzu basa cikin damuwa. Suna cigaba da harkokinsu na yau da kullum. Inji ta bakin mazauna garin sun ce jami'an tsaro basa matsa masu maimakon haka ma hakuri suke basu sabili da asarar da suka yi lokacin da 'yan Boko Haram suka dira kansu.
A Mubi mutanen kasuwa sun bude kantunansu suna gudanar da harkokin kasuwanci. Mutanen sun hada da kiran wadanda suka bar garin su dawo.
Babban asibitin garin Mubi bai tsira daga barnar 'yan Boko Haram din ba. A kofar asibitin an farfasa shaguna ana kuma fasa dakin da ake ajiye magunguna wadanda 'yan Boko Haram suka wawure.
A fadar sarkin Mubi Alhaji Abubakar Isa Ahmadu 'yan Boko Haram suka kafa tutarsu. Sun fasa wasu wurare a fadar kana suka yi awangaba da abun da suka kwashe. To amma yanzu alamura sun daidaita.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5